Wazirin Ilori, Bukola Saraki

Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ya taya sabon wazirin Ilori murnar sabuwar sarautar da Sarkin Ilori, Ibrahim Sulu Gambari ya bashi, inda aka daga darajar Bukola Saraki daga Turakin Ilori zuwa Wazirin Ilori.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta hannun mai magana da yawunsa, Abdulwahab Oba a ranar Lahadi a birnin Ilori na jihar Kwara.

Gwamna Abdulfattah ya bayyana wannan karin girma da Saraki ya samu a matsayin abinda ya dace ga wanda ya dace, duba da irin yadda shi Saraki ya bayar da gudunmawar ciyar da masarautar jihar gaba.

“Abin mai kyau kwarai da gaske irin yadda Saraki yake bin sawun mahaifinsa Abubakar Olusola Saraki wajen cin gajiyar irin wadannan sarautu.”

 

LEAVE A REPLY