Sabon Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha

Boss Gida Mustapha, shi ne mutumin da aka bayar da sanarwar naɗa shi a mukamin sabon sakataren Gwamnatin tarayya, bayan da aka bayar da sanarwar sallamar Babachir David Lawal daga aiki.

Shi dai mutumin da aka naɗa a matsayin sabon sakataren gwamnatin, kwararren lauya ne, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa.

Boss Gida Mustapha, ya taba rike mukamin mataimakin shugaban rusasshiyar jam’iyyar ACN, daya daga cikin jam’iyyun haɗakar da suka narke suka koma APC.

Kafin dai a bayar da sanarwar naɗa Babachir a matsayin sakataren Gwamnati tun farko wasu da dama sun yi tsammanin za’a naɗa Gida Mustapha ne tun farko, amma sai abin ya zzo da bazata.

Kafin naɗa Gida Mustapha a wannan sabon mukamin nasa, shi ne, Manajan daraktan hukumar NIWA mai lura da hanyoyin ruwa da na tsandauri na Najeriya.

Waye Boss Gida Mustapha?

An haifeshi a jihar Adamawa, ya halarci makarantar sakandire ta garin Hong dake jihar Adamawa, inda daga nan ya wuce zuwa makarantar share fagen shiga jam’ah ta yankin Arewa maso gabas dake garin Maiduguri, a jihar Borno a shekarar 1976.

Daga nan ya wuce zuwa jami’ar Ahamadu bello dake Zaria, inda ya samu takardar shaidar kammala digirin farko a fannin Lauya a shekarar 1979, inda ya shiga makarantar horon lauyoyi ta kasa a shekarar 1980.

daga shekarar 1980 zuwa 1981 Gida Mustapha yayi hidimar kasa, sannan daga bisani ya kama aiki da kamfanin “Sotesa Nigeria Limited”, wani kamfanin kwararruna turawan Italiya, a matsayin babban darakta mai lura da ayyukan gudanarwa na kamfanin, ya bar aiki da kamfanin a shekarar 1983, inda ya fara aiki da wata cibiyar Lauyoyi mai suna Messrs Onagoruwa a birnin Legas.

Daga nan kuma Boss Gida Mustapha yayi aiki da hukumomi da dama, ciki kuwa har da hukumar PTF wadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba shugabantar ta. Daga nan kuma, yana daga cikin mutanen da suka nuna hazaka lokacin da ya rike mukamin akawu a kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen jihar Adamawa.

Daga bisani, kuma ya shiga cikin al’amuran siyasa, inda har ya zama mataimakin shugaban rusasshiyar jam’iyyar ACN ta kasa. Wadda ta rushe don kafa jam’iyyar APC mai mulki, ya kasance mamba a kwamtin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a shekarar 2015.

bugu da kari kuma, yana daya daga cikin ‘yan kwamitin mika ragamar mulki daga PDP zuwa hannun jam’iyyar APC wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada su. Baya ga haka kuma, yana daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na jam’iyyar APC.

Boss Gida Mustapha Allah ya albarkace shi da iyali da ‘ya ‘ya, mutum ne mai san wasan kwallon lambu, da son tafiye tafiye musamman a cikin ruwa, da kuma son mu’amala da mutane.

LEAVE A REPLY