Masallacin da aka kai hari a Gamboru

A kalla mutu biyar ne suka rasa rayukansu, a safiyar yau lokacin da wata ‘yar karamar yarinya ta kai harin kunar bakin wake a wani Masallaci a kauyen Gamboru dake yankin karamar hukumar Gamboru-Ngala a jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar, lamarin ya auku ne da misalin karfe 5:00 na asuba, lokacin da ‘yar karamar yarinyar ta tayar da Bom din a cikin masallacin, an kuma ga yadda namanta yayi kaca-kaca.

Rogers Nicholas, Shugaban rundunar yaki ta Lafiya Dole, ya tabbatar  da NAN kai wannan hari a lokacin da yake zantawa da su a birnin Maiduguri.

Mista Nicholas, wanda Mejo Janar ne a rundunar Sojan kasa ta Najeriya, yace mutum biyar ne suka rasu a sakamakon wannan hari, ba mutum sha-daya ba kamar yadda aka fada da farko.

“Eh haka ne, amma mutum biyar ne suka rasu a wannan hari, kuma anci nasarar dakile kai wani harin a Rann, shalkwatar karamar hukumar Kala-Balge.

“Wani mazaunin garin na Gamboru, Lawan Abba, ya shaidawa NAN cewar, mutum goma ne suka mutu yayin da wajen shida suka ji munanan raunuka”

Abba ya bayyana cewar, ‘yar kunar bakin waken ta kutsa kai cikin masallacin ne a lokacin da mutane suke sauri domin su samu Sallah, sannan ta tayar da Bom din da ke jikinta.

Ya kara da cewar, yarinyar ‘yar kunar bakin waken, ‘yar asalin garin na Gamboru ce, domin kuwa mahaifin yarinyar yana daya daga cikin mutum goma dasuka mutu a sakamakon wannan hari.

“Yarinyar ta shiga cikin masallacin inda take masu ibada, ciki kuwa har da mahaifinta”

Abba ya kare da cewar, wadan da suka ji raunuka, an dauke su zuwa sansanin ‘yan gudun jihar dake yankin domin basu magani.

NAN

LEAVE A REPLY