Wata sabuwar Amarya a jihar Sakkwato ta kekketa sabon angonta da sabuwar reza. Amaryar mai suna Shafa Muhammad ‘yar Shekaru 28, ta hari sabon angon nata ne da sabuwar reza, inda ta ji masa munanan raunuka a fuskarsa.

Lamarin dai ya auku ne a unguwar Arkillar Liman da ke yankin karamar hukumar mulki ta Wamakko a jihar Sakkwato inda Amarya da Angon suka tare domin cin amarcinsu.

Wannan balahira tsakanin ango da Amaryarsa, ta faru ne sati uku bayana aurensu, a ranar 16 ga wannan watan na Disamba da muke ciki.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar, ita dai Shafa an tursasa mata auren angon nata Umar, abinda ya ci karo da zabinta.

“A lokacin da angon ya shiga dakin Amarya domin kashe dare, kawai Amaryar ta far-masa da reza a hannunta, inda ta yayyenke shi”

“Angon ya samu munanan raunuka a fuskarsa, sakamakon yankan da ta yi masa akansa da sauran fuskarsa” Wani makusancin iyalin ne ya tseguntawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, tare da fatan za’a sakaya sunansa.

A lokacin da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan Sandan Najeriya reshen jihar Sakkwato Ibrahim Abarass, yace, tuni aka yiwa angon jinya, kuma an sallame shi daga asibiti tunda ciwukan basu yi tsananin gaske ba.

Ibrahim Abarass, yace, tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta garkame Amaryar, kuma ana shirin gurfanar da ita daga zarar an kammala bincike.

Sannan kuma, ya shawarci iyaye da su daina tursasawa yaransu auren wadan da ba su ne zabinsu ba domin zamantakewar aure.

NAN

LEAVE A REPLY