Wasu Nakasassu a yayin zanga-zanga

Daga Ibrahim Abdul

Sakamakon abun da suka kira shakulatin bangaro da kuma kyamar da suka ce gwamnatin jihar Taraba na nuna musu kungiyoyin nakasassu a jihar Taraba,arewa maso gabashin Najeriya na barazanar cigaba da zanga-zangar lumana don neman a share musu hawaye.

Ko a makon jiya ma dai,sai da hadakar kungiyar nakasassu a jihar da suka hada da kutare,kurame,guragu,makafi da bebaye suka  karade birnin jihar wato Jalingo dauke da kwalaye suna nuna fushinsu tare da zargin cewa gwamnatin jihar ta maida su saniyar ware.

To sai dai wadannan nakasassun sun samu turjiya daga zaratan jami’an tsaron dake gadin gidan gwamnatin jihar   wadanda suka hana su shiga batun da ya tun zura su.

Yayin dai wannan  zanga-zangar lumana da suka gudanar a Jalingo  sun soma ne da  nuna kyamansu  ga barace-baracen da wasunsu keyi da kuma shakulatin bangaron da suke zargin gwamnatin jihar na nuna musu .

To sai dai kuma turjiyar da suka samu  daga zaratan jami’an tsaron dake gadin gidan gwamnati wadanda suka hana su shiga ya tun zura nakasassun,koda yake  da jibin goshi kwamishiniyar harkokin mata Malama  Loise Emmanuel wanda ta wakilci gwamnan jihar Arch.Darius Dickson Isiyaku ta shiga  tsakani.

Bayan da ta yi jawabinta  nema , sai shima sakataren kungiyar nakasassun jihar Aliyu Muh’d Dados dake cikin jagororin nakasassu a jihar yayi jawabinsa inda ya tabo matsalar baiwa nakasassu aikin yi.

Haka nan da yake jawabi ga manema labarai game da halin da suke ciki ayanzu, Aliyu Muh’d Dados yace zasu cigaba muddin gwamnati bata dube su da idon rahma ba.

A cewarsa, Makon jiya mun fito ne don nuna bacin ranmu game da halin ko –in-kula da ake nuna mana,kuma a gaskiya bamu jin dadi kuma ba zamu lamunce ba.

A baya mun gana da mataimakin gwamna,da sakataren gwamnatin jihar,kai harda kwamishinan ma’aikatan dake kula damu, to amma shiru kake ji.

Adon haka ne muk fito ,kuma gashi  an tare mu  tun daga kofar shiga.

Najeriya dai kasa ce dake da nakasassu da dama dake bara,koda yake mabaratanta ba wai kawai nakasassu ba,har da masu lafiya dake da mtuwar zuciya!

LEAVE A REPLY