Wata budurwa ‘yar shekara 17 mai suna Ramatu Tafida ta yankewa saurayinta mazakuta mai suna Abdullahi Sabo a jihar Jigawa a cewar hukumar tsaro ta NSCDC.

Kakakin hukumar AC Adamu Shehu shi ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaru na Najeriya, NAN, a babban birnin jihar Dutse, inda yace lamarin ya auku ne a yankin karamar hukumar Babura.

AC Adamu Shehu ya kara da cewar, mutumin da lamarin ya faru da shi mazaunin Kofar Gabas ne, wanda kuma malamin makaranta ne a makarantar ‘yan mata dake babura kuma daya ne daga cikin wadan da suka ci gajiyar shirin nan na N-Power.

 

LEAVE A REPLY