Wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba, sun kashe wani dan asalin kasar Siriya dake kasuwanci a Kano, Ahmed Areeda tare da sace dansa mai shekaru 14, Muhammad a jihar Kano.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar, lamarin ya auku ne a ranar Talata da misalin karfe 8:05 na dare, lokacin da mutanan da ba wanda ya gane su, suka bibiyi mamacin a inda yake ajiye motarsa a daura da ofishin hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross dake kan titin asibitin Nasarawa.

Bincike ya nuna cewar an harbi mamacin ne a kansa, a lokacin da yake cin karfin mutanan da suke yunkurin sace masa dansa.

Wani da abin ya faru akan idonsa, ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewar, maharan su 8 ne, sun kaiwa mutumin farmaki a lokacin da yaje daukar motarsa daga inda yake ajiye ta a harabar ofishin Red Cross dake kan titin asibitin Nasarawa.

Shaidun gani da idon sun kuma tabbatar da cewa, “Mamacin ya rufe shagonsa da yake kasuwanci da misalin karfe 8:00 na dare kamar yadda ya saba, daga nan ya tafi ya dauko motarsa a inda ya saba ajiyeta”

“Abinbakin ciki, maharan wadan da suka ajiye motarsu kirar fijo mai launin ganye a daura da inda mutumin ya ajiye tasa, suna jiran fitowarsa. Wasu daga cikin maharan sun bishi har inda yaje don daukar motarsa da yake akwai duhu, saura kuma suna daga waje”

“Wadan da suka bi mamacin dan asalin kasar Siriya, sun harbe shi akansa, sannan suka sungume dansa Muhammad” A cewarsa.

Wani shaidar kuma yace, dan mamacin na biyu, ya garzayo shagonsa a guje, yana shaida masa cewarwasu mutane sun kashe mahaifinsa, yake cewar “Ko da na garzaya wajen a guje, na samu ya mutu, sun harbeshi ta barin kunnesa inda harsashin ya shiga cikin kansa”

Da muka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da faruwar wannan lamari.

“Wannan abinda ya faru, maharan sun so su sace dan mamacin ne domin yin garkuwa da shi, a kokarin yin haka, da suka ga hakarsu ba zata cimma ruwa ba, shi ne suka kashe mutumin (Dan Siriya)” A cewar Magaji Musa Majiya

Har ya zuwa wannan lokaci babu wanda rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama kan wannan batu, sannan ba a san inda mutanan suka gudu da yaron da suka sace ba.

Amma kuma, ya tabbatar da cewar rundunar ‘yan sanda tana nan tana gudanar bincike dan gano maharan tare da gano yaron da aka sace din.

LEAVE A REPLY