Wasu mutum biyar sun shiga hannu sakamaon kama su da akai da laifin satar digar jirgin kasa da ta kai zunzurutun kudi har Naira miliyan 84.7, an kuma gurfanar da su gaban kuliya a kotun majastire dake Ebute Meta a jihar Legas.

Mutanan su ne, Mohammed Idris 22 da Idris Yusuf 36 da Mohammed usaini 25 da Sank Aliyu 21 da Abubakar Idris 19 sun bayyana gaban kuliya kuma an karanta musu laifukan da ake yuhumarsu da aikatawa wajen hadin baki don yin sata.

Dukkansu dai sun amsa cewar ba su aikata abinda ake tuhumarsu da aikatawa ba, yayin da ake karanta musu tuhumce tuhumcen da ake yi musu.

Mai gabatar da kara na kotun Moses Uamdevmbob ya shaidawa kotun cewar a ranar21 ga watan Mayu da misalin karfe 8 na safe suka aikata laifin a tashar jirgin kasa dake Mada a jihar Nasarawa.

Mai Shari’ah OA Komolafe ya bayar da belinsu akan kimar kudi Naira 500,000 kowannensu, tare da gabatarda wasu mutum biyu da zasu tsayawa kowannensu, kuma dole mutanan su kasance suna da aiki mai gwabi.

NAN

LEAVE A REPLY