Daga Hassan Y.A. Malik

Wata kotun majistare da ke zamanta a garin Minna, jihar Neja, a yau Juma’a ta yankewa wasu maza 3 daurin makonni 12 bisa samunsu da laifin satar kare.

Mutane ukun sun hada da: Isaac Saba, Philip Daniel da Ayo Ojo wadanda tun da fari aka gurfanar a gaban kotu ne bisa aikata laifuka biyu da suka hada da: hadin gwiwa wajen aikata laifi da kuma sata.

Mutanen dai basu wahalar da shari’a ba, inda nan take suka amsa laifinsu, wanda ya ci karo da sashe na 298 da 287 na kundin Panel Code.

Mai shari’a Hamza Mu’azu ya yankewa masu laifin hukunci bayan sun amsa laifukansu, inda ya ce, “Kowane mutum daya daga cikin masu laifin zai shafe makonni 4 a gidan kaso ko kuma ya biya tarar Naira 2,000.”

Tun da fari dai sai da mai shigar da kara, Sajan Aliyu Malami ya bayyanawa kotu cewa wata mai suna Mary Aliyu ta yankin Kpakungu na garin Minna ne ta shigar da kara a ofishin ‘yan sanda a ranar 3 ga watan Afrilu.

Sajan Malami ya ci gaba da cewa, Mary ta ce karen nata da wadancan mutane suka sace, darajarsa zai kai Naira 10,000.

LEAVE A REPLY