Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta shaida cafke wasu mutum biyu – Patrick Udom mai shekaru 35 da James Roland bisa zargin kashe makwabcinsu, Happy Patrick

An kuma zargin wadannan mutane biyu da sace mashin din mamacin kirar Bajaj bayan sun kashe shi tare kuma da boye gawarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni dai daya daga cikin mutum biyun da suka cafke ya amsa cewa sun kashe Happy Patrick ne kawai don su sace mashin dinsa.

An samu gawar Happy Patrick ne a yashe a daji kuma an samu addina biyu, guduma da wata wuka a inda suka jefar da gawar.

LEAVE A REPLY