Wani kamfanin jirgi a kasar Indiya ya sallami biyu daga cikin ma’aikatansa sakamakon kaurewa da fada da suka yi a lokacin da jirgin yake surfa gudu a sararin samaniya a farkon wannan shekarar, a yayin da jirgin ya taso daga birnin Landan na kasar Burtaniya zuwa birnin Mumbai na kasar ta Indiya.

Jirgin mai suna Jet Aireways, a wata sanarwa da ya fitar, yace har ya zuwa wannan lokacin ba su kai ga samun dalilin da ya haifar da fadan tsakanin matukan jirgin biyu ba.  Amma sai dai, rahotanni sun nuna cewardaya daga cikin matukan jirgin ya gallawa abokiyar aikinsa mari yayin da suke fadan.

“A sabida wannan abin kunya da suka yi, kamfani ya bayar da sanarwar korar wadannan mutane guda biyu daga aiki, kuma wannan kora ta fara aiki nan take” A cewar kamfanin jirgin.

Kamfanin dai bai yi wani karin haske ba dangane da aukuwarlamarin. Amma sai dai wasu kafafen yada labarai a kasar ta Indiya, sun ce, matukin jirgin namiji shi ne ya fara marin abokiyar aikinsa wadda macece a lokacin da aka jiyosu suna cecekuce.

Jirgin wanda yake dauke da mutane 324 a lokacin yana da ma’aikata 14, ya sauka lafiya ba tare da samun wata matsala ba. A cewar majiyar Fox.

LEAVE A REPLY