Wasu mata masu dauke da juna biyu da aka sauya su daga jihar Kwara zuwa sansanin horar da masu hidimar kasa dake jihar Oyo a Iseyin sun haihu, inda suka haifi ‘ya ‘ya mata a sansanin horas da masu hidimar kasar.

Jami’in dake kula da hukumar NYSC na jihar Oyo,Ifeoma Anidobi, ita ce ta bayyana haka a lokacin da take tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a birnin Badun.

Mis Anidobo ta kara da cewar, jariran an haife su a ranar alata, ranar farko da dalibai suka fara karbar horo domin yin hidimar kasa a rukuni na biyu na shekarar 2017.

“Jaririya ta farko an haifeta ne da sanyin safiyar talata a babban asibitin Iseyin, dayar kuma an haifeta da hantsi a dai wannan ranar”

“Iyayan jariran dukkan su masu yin hidimar kasa ne, da aka turo su daga jihar Kwara zuwa jihar Oyo domin karbar wannan horo na mwakanni uku”

“jami’ar dake kula da masu yin hidimar kasar ta yiwa Allah godiya da matan suka haihu lafiya lau ba tare da wata matsala ba”

NAN

LEAVE A REPLY