A wannan ziyara datsohon Gwamnan Kano kuma Sanata a yanzu, Rabiu Musa Kwankwaso zai kawo Kano, tana ta yamutsa hazo, a yayin da magoya bayan Kwankwaso ke ta kiraan Allah ya kawo Kwankwaso lafiya, wasu kuma na ganin Sanata Kwankwaso ya jingine batun zuwan nan nasa.

Da dama na tunanin za’a samu yamutsi tsakanin magoya bayana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da aka fi sani da ‘yan Kwankwasiyya da kuma magoya bayan Gwamna Ganduje da aka fi sani da ‘yan Gandujiyya.

A ranar 30 ga wannan watan na Janairu ne dai aka sanya ranar da shi Sanata Kwankwaso zai zo Kano din. Sai dai uni, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Rabiu Yusuf, ya rubutawa Sanata Kwankwaso wata wasika ta kashin kansa a ranar 19 ga wannan wata,inda yake rokon Kwankwaso ya janye batun zuwansa Kano.

Sai dai a wasikar martani da Sanatanya aiko zuwa ga shi Kwamishinan ‘yan sanda, rundunar ‘yan sanda ta Kano taki karbar wasikar da Sanata Kwankwason ya aaiko.

“Tun a ranar 19 ga watan Janairu, shima Kwankwaso ya aiko da tasa wasikar, amma a shalkwatar runudunar ‘yan sandan, aka bayar da umarnin duk wata takarda da ta fito daga wajen Sanata Kwankwaso kada a karbe ta” A cewar wani wanda yake bibiye da wannan lamari tsakanin bangarorin biyu.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto mun kasa samun, Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano,Magaji Musa Majiya ta wayar tarho domin jin ta bakinsa kan wannan batu.

Sai dai DAILY NIGERIAN ta samu kwafin wasikar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya aikewa da Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Rabiu Yusuf.

Sanana Kwankwaso ya fada a cikin wasikar, mai makon Kwamishinan ‘yan sanda ya bi bahasin abubuwan da ke faruwa, kawai yayi gaban kansa wajen kira ga Kwankwaso da ya jingine batun zuwansa Kano, a cewar Kwankwaso, shi da magoya bayansa, masu son zaman lafiya ne da bin doka.

LEAVE A REPLY