Shugaban tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari yayin da yake jawabi a kasar Ghana

Sanata mai wakiltar jihar Bayelsa ta gabas a majalisar dattawan Najeriya, Ben-Murry Bruce a ranar talata ya caccaki kalaman da Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari yayi a kasar Ghana.

Shugaba Buhari dai yayi alkawarin taimakawa kasar dake yankin yammacin Afurka yaki da cin hanci da rashawa, Buharin ya bayyana hakan ne a bikin cikar kasar Ghana shekaru 61 da samun mulkin kai a ranar Talata.

A lokacin da yake mai da martani kan kalaman na Shugaba Buhari, Mista Bruce yace, Shugaban tarayyar Najeriya kamata yayi ya fara nuna misali akan yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ba yakar ‘yan adawa ba ka dai.

A cewar sanatan, Shugaba Buhari ya sanya duniya na yiwa Najeriya dariya kan batun yaki da cin hanci.

Sanatan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter “Gara ka nunawa duniya yadda kake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, ba yakar ‘yan adawa ba”

“Idan har za’a ce al’amarin cin hanci na karuwa a Najeriya, zaka mayar da kanka abin dariya a idon duniya, idan kace wai zaka yaki cin hanci a wata kasa”

LEAVE A REPLY