Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufai

Wani masinja, mai suna Abubakar Shu’aibu dan kimanin shekaru 45, wana ke aiki a Makarantar sakandiren Gwamnati ta Aminu Marmara dake Sabongari Zarira, a jihar Kaduna. Abin ya faru ne ranar talata, inda mutumin ya fadi kasa sumamme bayan da aka bashi takardar sallamarsa daga aikin masinja.

Wani da abin ya faru a gaban idonsa, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewar, mutumin ya fadi kasa sumamme ne a sakamakon kaduwa da yayi daga korarsa da aka yi.

Yace, mutumin yana aiki a matsayin masinja kimanin shekaru 11 da suka gabata. “Mun isa wajen aiki da safe ni da Abubakar Shu’aibu, daga nan aka gayyace mu zuwa ofishin shiyya na ma’aikatar ilimi; mun isa wajen, aka mikawa Abubakar takadar sallamarsa daga aiki”

“Yana dawowa wajen aiki ya nunawa abokan aikinsa wasikar da ya karbo, daga nan muka bashi shawara ya dauki al’amrin a matsayin kaddara.”

“A lokacin da ya fadi sumamme, mun yi gaggawar bashi agaji, inda muka kama shi muka aje shi akan malale, muna danna shi muna yafa masa ruwa, har ya dawo hayyacinsa” A cewarsa.

Malaman da suke wajen, suka dauki alkawarin su yi karo karo daga albashinsu, domin su tara masa wani abu da zai yi amfani da shi dan dawainiyar gidansa.

Haka kuma, Malaman makarantar, sun roki Shugaban makarantar, Malam Sa’idu Liman-Umar da ya taimaki Malam Abubakar ya dauke shi a matsayin ma’aikacin wucin-gadi na dan wani lokaci.

“Nan take, Shugaban makarantar ya amince ya dauke shi a matsayin ma’aikacin wucin gadi ko me zai faru” A cewarsa.

Sai dai jami’an ofishin shiyya na ma’aikatar Ilimin yankin sun ki yin magana kan batun lokacin da aka nemi ko zasu mayar da martani kan lamarin lokacin da ‘yan jarida suka nemi su ce wani abu kan batun.

Haka kuma, Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kaduna bata yi wani karin bayaniba kan batun, haka itama Gwamnatin jihar Kaduna bata ce komai ba.

Sai dai idan za’a iya tunawa, Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai ya bayar da umarni duk wasu masu aikin goge-goge da masinjoji duk a sallame su daga aiki inda suka shekara 10 suna aiki kuma ba su da Difloma ko NCE a kalla.

LEAVE A REPLY