Wani matashin dan shekaru 26 mai suna Muhammad Suleiman, wanda Malamin makaranta ne ya yiwa wata yarinya ‘yar shekaru uku fyade, bayan da yayi mata wayo ya kaita cikin wani aji.

Lamarin dai ya faru ne a unguwar Rimin Gata dake yankin karamar hukumar Ungoggo a jihar Kano. Malamin dai na fuskantar tuhuma a gaban kotun majstire a Kano kan laifin yin lalata da karamar yarinya.

Sai dai kuma, da aka gabatar da Muhammad Sulamain a gaban kuliya kan zargin da ake yi masa,Malamin ya musanta aikata lalata da yarinyar. Inda ya bayyanawa alkali cewar sam bai aikata abinda ake zarginsa da aikatawa ba.

Mai gabatar da kara, Pogu Lale, ya bayyana cewar, Malamin ya yaudari ‘yar karamar yarinyar, zuwa wani ajin da babu kowa a ciki a ranar 13 ga watan Afrilu, malamin ya tara da yarinyar.

A cewar mai gabatar da kara, Pogu Lale, yace makarantar na nan a unguwar Rimin Gata dake yankin karamar hukumar Ungoggo.

Mai gabatarda karar ya cigaba da shaidawa kotu cewar, a ranar 14 ga watan Afrilu, mahaifin yarinyar ya shigar da koke a caji ofis din ‘yan sanda dake Rijiyar Zaki.

“Mutumin da ake zargi, ya tara da yarinyar, abinda ya janyo mata samun rauni a matancinta” A cewar sa, wannan laifi ya sabawaa sashi na 284 na kundin dokar final kod.

Babban majastare Muhammad Jibril ya bayarda umarnin a cigaba da tsare mutumin da ake zargi a gidan maza.

Sannan kuma, ya dage sauraren karar zuwa 24 ga watan Mayu maai zuwa.

NAN

LEAVE A REPLY