Wani Malami a makarantar jeka ka dawo ta Gwamnati dake Sankalawa a yankin karamar hukumar mulkin Bungudu dake jihar Zamfara ya yiwa wani dalibin mugun duka har dalibin ya sheka barzahu nan take.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaita cewar lamarin ya auku ne a lokacin da majalisar dokokin jihar ta sanar da faruwar abin a zamanta na ranar Laraba. Inda mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Muhammad Abubakar-Gummi ya sanar.

Mataimakin kakakin majalisar ya fadi haka ne a wani yanayi na nuna damuwa, inda yace ba Bungudu kadai ba, a makarantar ‘yan mata ta kwana dake Kwatarkwashi a yankin Gusau, an samu labarin wata malama ta baiwa daliba horo har sai da yarinyar ta samu raunuka.

Mataimakin yayi kira ga Kwamishinan Ilimin jihar ta Zamfara, da ya bayyana gaban majalisar dokokin jihar domin bayyana mata irin matakan da suke dauka domin magance irin wadannan matsaloli a jihar.

“Yin horo na rashin imani, ba wai cutarwa kawai yake yi ga dalibai ba, yana kuma sanya musu kyamar karatun boko, wanda wannan babbar illa ce ga ilimi a jihar Zamfara” A cewar Muhammad Abubakar Gummi.

NAN

LEAVE A REPLY