Hassan Y.A. Malik

Wani matashi dan kimanin shekaru 22 da haihuwa da aka bayyana sunansa da Lekan Olagunju ya samu hukuncin zaman gidan kaso na wata guda bayan da kotu ta same shi da laifin cin zarafin dan sanda ma suna Alayande muritala da wasu mata biyu, Florence James da ‘yar ta Victoria James.

A lokavcin sauraron karar, mai shigar da kara, furosukyutan ‘yan sanda, Sufeto Joshua Oladoye ya shaidawa kotu cewa, a ranar 5 ga watan Janairu, 2018 da misalin karfe 1:30, a kokarin shigarwa uban gidansa fada, Lekan ya ci zarafin Florence da ‘yarta Victoria.

Ko da aka turo dan sanda ya tafi da shi bayan Florence ta yi karar Lekan, sai ya rukumi dan sandan, inda haka ya yi sandiyyar lalata takalmin da agogon dan sanda da aka yi kiyasin darajarsu ya kai Naira duba 25.

Haka kuma an samu ganyen tabar wiwi a wajen Lekan a lokacin da ‘yan sanda suka ci karfinsa suka kama shi.

furosukyuta Oladoye ta ci gaba da cewa laifin da ake zargin lekan da shi ya saba sashen doka na 516 (A), da sashe na 356, da sashe na 70, da sashe na 430, da sashe na 249 (D) kuma dukkan sassan dokar jihar ta Osun sun yi umarni da hukunci ga wanda ya aikata laifin.

Wanda ake zargin, wanda a rana ta farko na zaman ya ki amsa laifinsa, a jiya Alhamis, ya amsa laifuka 6 da ake zarginsa da su.

Sai dai lauya mai kare wanda ake kara, Barista Najite Okobe ya roki kotu da ta yi wa Lekan Adalci kasancewar wannan ne karo na farko da aka taba samunsa da irin wannan laifin, haka kuma ya shafe wata guda a tsare a gidan kaso a lokacin yana jiran a yanke masa hukunci sakamakon beli da ya kasa biya.

Alkalin kotun, Mai shari’a O.A Ayilara, bayan sauraren koken lauyan wanda ake kara ya yankewa Lekan hukuncin daurin wata guda, sai kuma tunda ya shafe wata guda a tsari a lokacin da ya ke jiran a yanke masa hukunci, kotu ta umarci da wancan zaman gidan kaso da ya yi a matsayin hukuncinsa, inda nan take Mai shari’a Ayilara ya umarci da Lekan ya tafi.

LEAVE A REPLY