Daga Hassan Y.A. Malik

Wani matashi mai shekaru 17 da haihuwa da aka bayyana sunasa da Mahmud Adamu ya rasa ransa a hannun yayansa, Nura Adamu mai shekaru 19 da kuma dan uwansa, Hussaini Adamu bisa zarginsa da satar wayar hannu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja, Muhammad Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a garin Minna, inda ya ce Nura da Hussaini da a yanzu ba a gano inda suke ba sun yi wa dan uwansu dukan kawo wuka ne, kuma suka tsere suka barshi kwance cikin jini male-male.

 Kakakin ya ci gaa da cewa, “Gwajin asibitin da aka yi akan marigayi Mahmud ya tabbatar da cewa mutuwar tasa ta biyo bayan dukan tsiya da aka lakada masa ne.”

‘yan sanda sun dukafa wajen gano inda Nura da Hussaini suke don yi musu hukunci daidai da laifin da suka aikata.

LEAVE A REPLY