Fasto Tunde Bakare

Fasto Tunde Bakare mai lura da cocin Latter Rain Assembly ya kirawo ruwa, ta hanyar alakanta yunkurinsa na tsayawa takarar Shugaban kasa da cewar wahayi ne akai yi masa ya tsaya takarar Shugaban kasa.

Fasto Tunde Bakare shi ne tsohon dan takarar mataimakin Shugaban kasa karkashin rusasshiyar jam’iyyar CPC, wadda Shugaba Buhammadu Buhari ya yiwa takara a shekarar 2011 tare da Fasto Tunde Bakare a matsayin mataimaki.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwwaito, Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewar, Ubangiji ne yayi masa wahayin kada ya bari siyasarsa ta zo karshe face ya tsaya takarar Shugaban kasar Najeriya.

Bakare ya bayyana karara cewar Ubangiji ne ya umarce shi da fitowa takarar Shugaban kasa. Shehun malamin addinin kiristan ya bayyana hakan ne, a ranar litinin da daddare a lokacin da suke sujjada a cocinsa dake birnin ikko.

Daga cikin abubuwa 12 da Ubangiji yayi min wahayinsu, har da batun tsayawa ta takarar Shugaban kasa da zan kaddamar a wannan Shekarar ta 2018. Bakara ya kara da cewar, Ubangiji bai ayyana masa a yaushe zai zama Shugaban kasar ba, amma dai ya yi masa wahayin ya tsaya a wannan lokacin.

“Wannan daya daga cikin wahayin da aka yi min, nayi ta kokarin na barshin sirri tsakanina da Ubangiji ne, amma abin yaci tura, domin umarni ne aka bani na bayyanar da shi, babu kuma yadda zan tsallake maganar Ubanjigi”

“A lokacin da nake zaune nake wuridi da tsakar dare misalin karfe 4 na dare, Ubangiji ya sauko ya gaya min cewar, ‘Lallai ka sani ya kai Bakare siyasarka ba zata zo karshe ba, har sai kayi takarar Shugaban kasa, kuma ina mai umartar ka da ka tsaya takar’ inji bakare”

Bakare ya kara da cewar, “na san wannan wahayin da aka yi min shi, idan na bayyana mutane da yawa zasu ce karya nake yi, wasu ma zasu yi Allah wadai da abinda na fada, suce karya ce kawai na sharara, amma dai ko me zasu ce sai dai su fada, tunda Ubangiji ne yayi min wahayi”

“A cikin Linjila, an gaya mana cewar, Joseph bai nemi ya zama Shugaban kasar Masar ba, amma kuma sai Ubangiji ya mayar da shi Shugaban kasa. A saboda haka babu wani abu da zai sa na damu kaina, domin nasan alkawarin Ubangijina a gareni gaskiya ne”

Haka kuma, Bakare ya kara da cewar “Ubangiji na ya umarce ni da na yawaita adduah a gareshi, har lokacin da zai cika min wahayi na, ya mayar da ni Shugaban kasa a lokacin da yaga dama” A cewar Fasto Bakare.

Bakare ya kara da cewar, “Wanda duk suke jin sune manyan ‘yan siyasa da wadan da suka isa, zasu kare karkashin wata mace a 2018 dinanna”

“A shekarar 1998 na taba gaya muku cewar an yi min wahayin mutuwar Shugaban kasa, zai mutu tsakanin wasu ‘yan mata guda biyu, kuma hakan ta tabbata, A sabida haka, a yanzu ma da nake gaya muku wannan wahayin ku gasgata ni domin abinda na fada zai tabbata” Inji Fasto Tunde Bakare.

 

LEAVE A REPLY