Hassan Y.A Malik

Wani uba da dansa sun shiga hannun ‘yan sanda a sakamakon zargin su da ake yi da sayarwa yara ‘yan makarantar firamare miyagun kwayoyi a ciki har da Tramadol da Tramol.

Dubun uban mai suna Ibrahim Sheu da dansa Franku Ibrahim mai shekaru 23, ta cika ne bayan da jami’an hukumar tabbatar da inganciin ilimi ta jahar Lagos suka ziyarci wasu daga cikin makarantun suka kuma samu rahotan wasu irin dabi’u maras kan gado da wasu daga cikin yaran suke nunawa.

Jami’an sun yi gaggawar kai rahotan wannan lamari ga hukumar ‘yan sanda, inda ita kuma ta shiga bincike.

An kama uba da da a ranar 2 ga watan nan na Maris a shagonsu na sayar da kaya a yankin Itire da ke jahar Lagos.

An gano cewa mutanen 2 sun jima suna yin wannan muguwar sana’a kuma ba yara kanana kawai suke sayarwa kwayoyin ba har da manya.

An samu kwayar Tramadol guda 72 da ta Tramol 28 a gurinsu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legos, yayin da ya ke tabbatar da tsare mutanen biyu, ya shawarci iyaye da su dinga kulawa da halin da ‘yaran su suke ciki a makarantun su da ma irin abokan da suke ajiye wa.

LEAVE A REPLY