Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

‘Yan Najeriya mazauna Saudiyya da aka fi sani da Tukari, sun shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taimaka ya samarwa da yaransu makarantun da zasu yi karatun boko a kasa mai tsarki.

Da yake tattaunawa da manema labarai ranar Alhamis a birnin Madina, Shugaban kungiyar ‘yan najeriya mazauna Saudiyya ya bayyana cewar, da yawan yaransu basa samun ilimin boko a kasar Saudiyya.

Shugaban kungiyar Jaliyya Nijeriyyah Fi Madinatul Munawwara Tijjani Ali a matsayinsa na Shugaban kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Saudiyya ya ceidan aka samar musu da makarantun, ba shakka yaransu zasu samu ilimin boko wanda yake da karanci matuka a kasar ta Saudiyya.

Ya kara da cewar kasashe kamar su Chadi da Mali da Pakistan tuni suka samarwa da ‘yan kasashensu makarantu wanda hakan take taimaka musu sosai, yace suma suna da bukatar hakan, ko dan gudun bacewar harshen gida a tsakanin yaran nasu.

 

LEAVE A REPLY