Marigayi Hassan Lawal

Daga Hassan Y.A. Malik

Tsohon ministan ayyuka da gidaje kuma tafidan Keffi, Hassan Lawal ya rasu cikin daren jiya Asabar a wani asibiti mallakar kasar Turkiyya da ke Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Majiyarmu ta bayyana cewa za a yi jana’izarsa da safiyar yau Lahadi a garinsu da ke karamar hukumar Keffi, jihar Nassarawa kamar yadda shari’ar musulunci ta tanadar.

Hassan Lawal ya taba kasancewa ministan kwadago, ministan lafiya da kuma ministan ayyuka da gidaje.

Ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya da ‘yan uwa.

LEAVE A REPLY