Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya kuma shugaban rundunar sojojin kasa Victor Malu ya mutu. Malu ya mutu ne a yau, tuni dai shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya aikewa da iyalansa da sakon ta’aziyar rashinsa.

Shugaban ya aike da sakon ta hannun mai taimaka masa ta harkar yada labarai Mista femi Adeshina. Shugaban ya jinjinawa irin kokarin da Malu yayi, musamman ya tuno da gudunmawarsa yayin da ya jagoranci rundunar ECOMOG domin kawo zaman lafiya a kasar Laberiya a shekarun 1996 zuwa 1998.

Shugaba Buhari ya nuna juyayinsa tare da mika ta’aziyarsa zuwa ga iyalai da al’ummar jihar benuwai da kuma rundunar sojin Najeriya.

Shugaban ya kuma yi adduah ga iyalan Malu da su zama masu juriya da kamewa a yayin wannan babban rashi da suka yi. Yace su dinga tuna shi musamman ta sadaukarwar da yayi wajen tabbatar da zaman lafiya a najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.

LEAVE A REPLY