Marigayi Cif Jojin Najeriya, Dahiru Musdapha

Allah ya yiwa tsohon Cif Jojin Najeriya, Dahiru Musdapha rasuwa yana mai shekaru 75. Musdapha ya rasu a jiya talata a kasar Burtaniya sakamakon wata gajeruwar jinya da ya sha fama da ita.

an nada Dahiru Musdapha a matsayin Shugaban alkalan babbar kotun koli ta Najeriya a ranar 27 ga watan Augustan 2011, wanda tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rantsar da shi.

Dahiru Musdapha ya taba zaman Cif Joji a jihar Kano tsakanin shekarun 1979 zuwa 1985. Shi haifaffen garin Babura ne dake jihar Jigawa, ya rasu ya bar mace daya da ‘ya ‘ya uku.

 

 

LEAVE A REPLY