Wasu mutum biyu sun gamu da ajalinsu sakamakon wata tsawa da ta auka musua ranar juma’a a kauyen Pogo dake yankin karamar hukumar Paikoro a jihar Neja.

Aliyu Salihu dan shekaru 25 da kuma wani yaro dan shekaru 13 mai suna Abbas sun gamu da ajalinsu a lokaacin da ake tafka ruwan sama da misalin karfe8 na dare a ranar Juma’ar, inda akai wata tsawa mai karfi nan take kuma suka ce ga garinku nan.

Haka kuma,wani da aka bayyana sunan da Abdullahi ya samu rauni sakamakon fadowar aradu lokacin da akai wannan tsawa. Mahaifin Aliyu da ya rasu, ya bayyana cewar, dan nasa ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake roron mangwaro, inda lokacin tsawar ta fadawa garin ta yi awon gaba da shi.

“Abin ya faru kamar jan da wutar lantarki take yiwa mutum, duk mutanan kauyen sunji wannan jan da tsawa tai musu.”

“Lokacin da akai tsawar, naji ihun mutane a kofar gidana, bayan da ta lafa na garzaya a guje na tarar da mutum uku kwance shame shame, yace Aliyu da Abbas sun rasu nan take, yayin da Abdullahi yaji raunuka a jikinsa”

Mahaifin yaron ya nuna wani rami, yace inda nan ne yaraon nasa ya gamu da ajalinsa a lokacin da ake kyautata zaton aradu ce ta fada musu lokacin da akai wannan tsawa.

Mahaifin ya nuna matukar kaduwa da rasuwar dan nasa, inda yace suna ta kokarin ganin yayi aure nan kusa, ashe ajali na gab da riskarsa.

LEAVE A REPLY