Rahotanni daga yankin mazabar dan majalisar dattawa a yankin Katsina ta Arewa, na nuna cewar an samu fitowar jama’a sosai domin kada kuri’arsu a zaben cike gurbi da ake yi a yau Asabar.

Haka kuma, bayanai na cewar an tsaurara tsaro sosai a yankin da ake gudanar da wannan zabe. Har ya zuwa yanzu dai ba’a samu wani rahoton tashin hankali ko wani abu mai kama da haka ba a wajen zaben.

Mazabar dan majalisar  dattawa ta Katsina ta Arewa ita ce mazabarShugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ake zaben cike gurbin dan majalisar dattawa, domin maye gurbin Sanata Mustapha Bukar wanda Allah ya yiwa rasuwa a kwanakin baya.

 

LEAVE A REPLY