Wasu daga cikin jami'an Gwamnatin Buhari yayin da suke dakon zuwansa jihar Nassarawa

An jibge tarin jami’an tsaro a manya manyan tiunan birnin Lafiya, a yayin da ake sa ran zuwan Shugaba Buhari jihar domin gudanar da ziyara ta kwana daya.

Ana ganin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro cikin shirin ko ta kwana, a kusan ko ina a babban birnin jihar.

Haka kuma, a sauran garuruwa da suka hada da Akwanga da Keffi da kuma Karu duk ana ganin tarin jami’an tsaro a manyan titunan garuruwan.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Nassarawa, Bello Ahmed, ya shaida cewar fiye da ‘yan sanda 4,000 aka jibge domin zuwan Shugaba Buhari a yayn wannan ziyara ta yini guda.

 

LEAVE A REPLY