Daga Fatuhu Mustapha

Ance wata rana ana zaune a fada, sai sarkin Kano ya lura da Sarkin Yaki Muhammadu Dutsen Gima yana gyangyadi, sai sarki ya kalli Shamaki Dan Indo ya kalli Sarkin yaki, nan da nan Shamaki ya daga murya, yace “sarkin Yaki sarki yace kana bacci a gabansa!!” Ai nan da nan fadawa suka dauka “hattara sarkin Yaki! Baa bacci a gaban sarki!!”. Sarkin Yaki ya farka firgigi!!

Can akayi bisa ga kyau! Sarki yana mikewa yace “Sarkin Yaki ” nan da nan fada ta dauka “ka amsa kira sarkin Yaki “. Ya karasa ya fadi gaban sarki, sarki yace “yanzu Sarkin Yaki ba zaa saurara a ringa samu ana bacci da dare ba?”

Sarkin Yace “Allah ya taimaki sarki, ina zaayi bacci, bayan rayuwar Mata’un Qalilan ce”

Dutsen Gima dan Ibrahim!
Na Garba Mara bada abinci
Dan Amadu rumfar hanji
Wa zata taba ta zubo mai….

Ance kowaye kai, baka isa kace ka taba ganin Dutsen Gima na bacci da dare ba, saboda tsabar ijtihadi!!

Allah ya jikansu da rahama!!

LEAVE A REPLY