Sanata Ahmad Makarfi

Tsohon Shugaban riko na jam’iyyar PDP, Ahmad Makarfi yayi tir da abinda ‘yan sanda suka yiwa Shugabannin majalisar dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Ekweremadu, inda ‘yan sanda suka yi amfani da karfi domin hana su walwala.

Idan baku manta ba, Daily Nigerian ta ruwaito muku cewar, da sanyin safiyar Talata ne ‘yan sanda suka yiwa gidan Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da na mataimakinsa Ike Ekweremadu kawanya.

Rundunar ‘yan sanda ta kasa da jami’an hukumar tsaro ta fararen kaya da kuma jami’an hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC su ne suka kasa suka tsare suna jiran su yi ram da Shugaban majalisar  dattawan akn zargin da ake masa na hannu a fashin Offa da aka yi a jihar Kwara.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan abinda ya faru, ta hannun mai magana da yawunsa, Mukhtar Sitajo, Makarfi ya bayyana abinda ya faru da cewar yana da matukar hadari ga tsarin demokaradiyyar kasarnan.

 

LEAVE A REPLY