TY Danjuma

Daga Hassan Y.A Malik

Tsoho ministan tsaron Nijeriya, Theophilus Danjuma ya yi kira ga ‘yan Nijeriya gaba daya kpata, musamman ma al’ummar jiharsa ta Taraba da su tashi to kare kansu daga kisan kare dangi daga wata kabila.

Tsohon janar din sojan na yin nuni ne ga kashe-kashen da fulani makiyaya ke yi musamman a yankin arewa ta tsakiya.

Danjuma ya yi wannan bayani ne a wajen taron bikin yaye dalibai karo na farko na jami’ar jihar Taraba da aka gudanar jiya Asabar a Jalingo, babban birnin jihar ta Taraba.

Danjuma ya kwatanta kashe-kashen na fulani makiyaya akan al’ummatai a jihar ta Taraba a matsayi kokarin shafe wata kabila daga doron kasa, wanda dole mutane su tashi su kare kansu daga faruwarsa.

“Dole ku tashi ku kare kawunanku daga wadancan mutane domin kuwa in kuka dogara da jami’an tsaron kasar nan, to za ku mutu ne kawai a banza.”

“Wannan kashe-kashe na kare dangi dole ya tsaya haka a Taraba, kuma dole a kawo karshens a fadin Nijeriya.”

“Masu aikata kashe-kashen nan na samun kariya daga sojojijn Nijeriya, su suke boye su, saboda haka ya zama dole ku zama a ankare, sannan ku dauki damarar kare kanku.”

“Dole a dakatar da wannan kashe-kashen in ba haka ba abinda ya ke faruwa a kasar Somalia zai zama ba komai bane in aka kwatanta da abinda zai faru a Nijeriya muddi kashe-kashen nan bai tsaya ba.”

“Ina mai yi muku nasiha da ku kasance a ankare, ku tsare kasarku, ku tsare jiharku,” inji Theophilus Danjuma.

LEAVE A REPLY