Hassan Y. A. Malik

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, a yau Juma’a ya shigara da kara a kotu, inda ya nemi kotu da ta bi masa hakkinsa na kage da ya zargi Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi masa.

Gwamna El-Rufa’i dai da kansa ya shigar da karar a babbar kotun jihar Kaduna bisa abinda ya kira cin zarafi da kage da cin fuska da Shehu Sani ya yi masa ta kafofin sadarwa na yanar gizo.

El-Rufa’i ya a kunshin karar ya ce, Sanata Sani ya kira shi da bugagge (mashayin barasa), maketaci kuma maras wata kima a tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari.

Cikin abubuwan da Gwamna El-Rufa’i ya nema daga wajen kotu har da batun kotu ta shellatawa duniya cewa abubuwan da Sanata Shehu Sani ya fada game da shi ba gaskiya bane kuma ba halinsa bane.

Lauyan Gwamna El-Rufa’i, Barista Abdulhakeem Mustapha SAN, a yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a farfafajiyar kotun, ya ce, “Mun bukaci Naira dubu dari biyar a kan kowane sharri daya da ya yi mana.”

Ya kuma kore wannan tunanin da mutane ke yi na cewa gwamna bashi da ikon yin karar mutanen da ya ke mulki a jiharsa.

LEAVE A REPLY