Daga Hassan Y.A. Malik

An tashi baran-baran a taron gwamnati da gamayyar kungiyoyin ma’aikatan lafiya (JOHESU), kamar yadda wani shugaban kungiyar ya shaida.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Ogbonna Chimela, ya ce a taron da suka yi ranar Laraba, gwamnatin ta ce za ta ba su wani zabi da ba su sa ko mene ne ba.

“Sun ce za su bamu zabi amma ba mu san mene ne zabin ba. Dole sai mun gani sannan mu san ko abin da za mu yarda da shi ne ko a’a,” inji Mr. Chimela.

Kungiyar JOHESU, wacce kungiya ce ta ma’aikatan lafiya amma banda likitoci, na cikin yajin aiki na tsawon kwanaki 22.

A sakamakon haka, marasa lafiya na shan matukar wahala yayin da ungozomomi suka kukkulle na’urori a ma’aikatun lafiya na tarayya.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa an baiwa ma’aikatan na matakin jaha da kananan hukumomi umarnin bin sahu wajen shiga yajin aikin ranar Laraba da daddare.

Shugabannin kungiyar a matakin jaha da kananan hukumomi sun amince da shiga yajin aikin domin matsa wa gwamnati lamba ta biya masu bukatunsu.

Al’amura dai na cigaba da rincabewa saboda marasa lafiya ba da samun kulawa a asibitocin tarayya.

 

LEAVE A REPLY