Masallacin Ibrahim Bulbula-Koki

Image may contain: 1 person, sitting, beard and indoor

An bude wani Masallaci a Kano da aka fi sani da sunan Masallacin Ibrahim Bulbula-Koki, wani Masallaci da aka fi shekaru 20 ana takaddama akansa a unguwar Koki dake cikin birnin Kano.

Image may contain: 2 people, people standing and indoor

Shugaban kungiyar Izala ta jihar Kano, Sheikh Dr. Abdullah Sale Pakistan da Imamu Ahlussunnah Wal-Jama’a Sheikh Abdulwahab Abdallah da kuma Sheikh Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo su ne suka jagoranci kaddamar da bude wannan Masallaci mai dumbin tarihi a tafiyar kungiyar Izala a jihar Kano.

Image may contain: 11 people, people smiling, crowd

A yayin da yake jawabi wajen bude wannan Masallaci, Sheikh Dr. SAni Umar Rijiyar Lemo ya yi bayanin tarihin kafuuwar addinin Musulunci, yadda ya fara bako ana tsangwamarsa, har ya kawo yadda yake a yanzu.

Image may contain: 2 people, people standing and indoor

“Addinin Musulunci ya fara ne ana tsangwamar Musulmi idan zasu yi ibada, a haka, Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya dinga karfafa guuuiwar Sahabbai yana mai basu hakuri har addinin Musulunci ya kafu” A cewar Dr. Sani Rijiyar Lemo.

Shi dai wannan Masallaci wani mutum ne da ake kira Alhaji Ibrahim Bulbula dake unguwar Koki a cikin birnin Kano ya kuduri aniyar gina shi, tun kusan shekaru 30 da suka gabata. Ginin Masallacin a wancan lokacin ya gamu da cikas, kasancewar shi Ibrahim Bulbula yana tare da ‘yan Izala, inda mazauna unguwar dake bin darikun sufaye suka hana gina shi.

Tun fiye da shekaru 30 ake ginin Masallacin ana rusawa, har Allah ya yiwa Ibrahim Bulbula rasuwa ba tare da yaga kafuwar wannan Masallaci ba, sai a wannan lokaci shekaru 30 bayan an sha gwagwarmayar gina shi ana samun cikas daga mabiya darikun sufaye.

Da yake nasa jawabin, Dr. Abdallah Pakistan yace “Da yawan wadan da suka yi adawa da ginin wannan masallaci a baya, yanzu ‘ya ‘yansu ne suka tsaya kai da fata wajen ganin an tabbatar da ginin masallacin”

LEAVE A REPLY