Gwamnan jihar Taraba, Darius D. Ishaku

Gwamnatin jihar Taraba ta sanya dokar hana shiga da fita a Mayo Ndaga a yankin karamar hukumar Sardauna, bayan barkewar wani sabon rikicin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 29, tsakanin kabilun Mambila da na Fulani tsakanin matasan yankin.

Dokar da Gwamnatin jihar ta sanya a yankin ta fara aiki nan take, yayin da rikicin ya fantsama zuwa wasu sassan kauyikan da ke da makotaka da yankin da rikicin ya fara aukuwa.

Harin ya watsu zuwa yankunan Yarimeru da Kakara da mayo Ndaga da Sheri har da wasu yankuna dake da makwabtaka da iyalar Najeriya da kasar kamaru.

Shugaban karamar hukumar Sardauna, Godwin Sol, ya bayyana cewar an samu gawarwakin a kalla mutane 29, yayin da wasu da dama aka neme su aka rasa.

Haka kuma, an samu tabbacin cewar, a birnin Jalingo, Gwamna Darius Ishaku ya jagorancin wani zama na gaggawa da hukumomin tsaron dake jihar da ya hada da kwamishinan ‘yan sanda, David Akinremi da Shugaban hukumar SSS da dukkan sauran jami’an tsaro dake jihar.

Babban mai taimakawa Gwamnan ta fuskar yada labarai Mista Bala Dan Abu, ya tabbatar da wannan zama na gaggawa da Gwamnan yayi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar, sai dai babu wata sanarwa da aka fitar a hukumance dan gane da wannan taron.

Haka kuma, an samu rahoton cewar a lokacn wannan tattaunawa ta gaggawa, an bukaci a tura karin jami’an tsaro dukkan wani yanki na Tsaunin Mambila domin dawo da doka da oda a yankin, tare da tabbatar da cewar an kama duk wanda suke da hannu wajen tayar da wannan tarzoma.

Kakakin rundunar ‘yan Sanadan jihar Taraba, ASP David Misal, bai dauki kiran wayar da aka dinga yi masa ba, amma dai mai aiko mana da rahoto daga yankin yace, kakakin ya aiko da sakon tes inda yace yanzu haka “an samu dawowar zaman lafiya a yankin”/

Ko a satin da ya gabata an samu bullar tashin hankali a yankin ranar Larabar da ta gabata, inda aka kaiwa wasu yankunan Fulani hare hare a Yarimeru daga wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan kabilar Mambila ne.

LEAVE A REPLY