Daga Bilya Yariman Barebari
Maigirma gwamna Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal cfr mutawallen sakkwato ya jagoranci zaman tattaunawa na musamman da masu ruwa da tsaki da suka mara masa baya suka koma jam’iyyar PDP a wannan jiha.
Da yake jawabinsa a madadin mahalarta wannan taro, shugaban hukumar alhazzai na jiha, kuma daya daga cikin jigon siyasar wannan jiha, Alh Mukhtar Maigona yayi godiya ga Allah daya gwada muna wannan haduwar da zata kawo ciga ga wannan jam’iyyar ta PDP da muka koma dama jiha da kasa baki daya.
Maigona ya tabbatar ma maigirma gwamna tambuwal cewa da yardar Allah zasu cigaba da bada goyon bayan su 100% domin samun nasarar wannan tafiyar kamar yadda suke iya kokarin su a jam’iyyar da suka fito, inda ya bayyana cewa wadannan Shuwagabannin jam’iyyar da suka mara wa maigirma gwamna baya sune ke iya kokaarin samun nasara a dukkanin zabukan da ake ci a jam’iyyar da suka baro.
Maigirma gwamna Tambuwal yayin jawabinsa a wannan taron, yayi matukar nuna jin dadinsa ga Allah SWA daya gwada masa wannan ranar ta tattauna muhimman abubuwan da zasu kawo ci gaba ga wannan Jam’iyar ta PDP dama al’umma wannan jiha da kasa baki daya. Kuma yayi godiya ga Ilahirin al’ummar wannan jiha kan goyon baya da fatan alkhairi da suke bashi yayin gudanarda wannan mulki.
Maigirma gwamna yayi kira ga mahalarta wannan taron dasu cigaba da bada goyon baya ga wannan jam’iya ta PDP domin samarda ingantaccen cigaban rayuwar al’umma, dakuma kokarin wanzar da zaman lafiya ga al’umma a dukkanin lokuttan da za’a tun kara na siyasa. Inda yayi kira ga al’umma da su kara bada goyon baya ga wannan tafiyar domin cigaban wannan jiha. Da karshen yayi godiya ta musamman ga Ilahirin al’umma wannan jiha dakuma magoya bayan wannan jam’iyyar ta PDP kan goyon baya da fatan alkhairin da suke masa dakuma jiha baki daya.
Wannan zaman ya samu halartar masu ruwa da tsaki a wannan tafiyar ta PDP a matakin jiha, dakuma kananan hukumomi 23 dake garemu a wannan jiha, yan siyasa, tsofaffin kwamishinonin wannan jiha, masu baiwa gwamna shawara, mataimaka na musamman ga maigirma gwamna, da sauran muhimman mutane.

LEAVE A REPLY