Sanata Aliyu Wamakko

Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato kuma Sanata a yanzu a majalisar dattaan Najeriya, Aliyu Magatakarda Wamako ya bayyana ra’ayinsa kan ficewar da Gwamnan jihar mai ci Aminu Waziri Tambuwal yayi daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

Wamako ya bayyanawa wakilin gidan rediyan BBC Hausa, cewar, har yanzu Tambuwal yaro ne a siyasa kuma yana da kuruciya, ba dan yayi gaggawa ba da siyasarsa zata yi kyau nan gaba.

Haka kuma, Sanatan ya bayyana cewar har yanzu mutanan jihar Sakkwato suna tare da jam’iyyar APC da kuma SHugaban kasa Muhammadu Buhari.

LEAVE A REPLY