Kungiyoyin sa kai na sanya ido akan zaben Gwamnan jihar Ekiti sun yi watsi da sakamakon da hukumar zabe ta kasa ta fitar kan zaben Gwamnan Ekiti da aka yi a makon da ya shude. Inda aka bayyana Kayode Fayemi na jam’iyyar APC a matsayin wanda yaci nasarar lashe zaben.

A wata sanarwa da suka rabawa ‘yan jaridu, masu sanya idon sun bayyana cewar sakamakon da aka sanar ya sha bamban da ainihi abinda suka gani a zahiri. Sun bayyana cewar zasu fitar da sanarwar sakamakon da yake hannunsu a ranar Laraba mai zuwa.

Sanarwar wadda Shugaban gamayyar masu sanya idon Kwamared Haruna Farouk ya sanyawa hannu, ya bayyana cewar sakamakon da aka fitar abin kaico ne kwarai, ace Kwamishinan zaben hukumarzabe ta kasa ne ya sanar da hakan.

Ya kara da cewar, an yi amfani da jami’an tsaro da kuma hukumar zabe wajen canza ainihin abinda mutanen Ekiti suka zaba, a zaben Gwamnan na shekarar2018.

Gamayyar ta bayyana cewartana da cikakkun hujjoji da suke bayyana da yadda aka tafka kazamin magudi a zaben Gwamnan na Ekiti, inda suka bayyana sakamakon da abin takaici mai muni.

 

LEAVE A REPLY