Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincikar lamarin wata mata mai shekaru 47, wacce ake zargi ta kashe mijinta, ta hanyar farke cikinsa tare da yin waje da ‘yayan hanjisa, kana daga baya kuma ta yanke mazakutarsa.

Matar mai suna Udeme Odibi dai  yar jihar Legas ce.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin ta aikata laifin ne akan maigidanta mai suna Mista Otike Odibi mai shekaru 50 a gidansu da ke unguwar Diamond Estate a yankin Sango-Tedo.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ya fitar, ya ce an cafke matar lokacin da take yunkurin kashe kanta.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce a ranar 3 ga watan Mayu, ‘yan sanda sun samu bayanan cewa an kashe Otike a gidansa, kuma ana zargin matarsa ce ta aikata haka.

“Bayan samun wannan bayani, an tura jami’an ‘yan sanda wajen, inda suka samu gawar kwance cikin jini kaca-kaca, cikinsa a farke kuma hanjinsa a waje.

“Hakan bai isa ba, har sai da matar ta wuka ta yanke azzakarinsa, sannan ta ajiye a hannunsa na dama.”

Rahotanni sun bayyana cewa Otike ya auri Udeme ne shekaru 3 da suka gabata, kuma ta aikata wannan abu a kan shi ne saboda ta bukaci ya rubuta wasiyyar da zai sanya ta ta gaje shi ita kadai, lamarin da Otike ya ki yarda, saboda ya na da ‘ya guda daya daga auren shi na baya.

 

LEAVE A REPLY