Marigayi Sule Gaya

Allah ya yiwa tsohon Ministan ayyuka a zamanin jamhuriya ta farko, Aalhaji Sule gaya rasuwa yana da shekaru 93 a duniya.

Daya daga cikin iyalansa Hajiya Binta Gaya ita ce ta bayar da labarin rasuwar tasa ranar Alhamis da maraice.

An haifi Alhaji Sule gaya a shekarar 1925 a garin gaya dake jihar Kano, tsohon dan siyasa kwararren dan boko ne a zamaninsa.

An zabe shi a matsayin mamba a majalisar kasa a shekarar 1956, inda daga bisani ya zama magatakardar majalisar baki daya a shekarar 1957.

Haka kuma, an nada shi a matsayin kansla mai lura da sha’anin ilimi a hukumar NA ta wancan lokacin.

Kafin rasuwarsa yana rike da Sarautar Sarkin Fadar Kano.

LEAVE A REPLY