Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki

Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewar Sufeton ‘yan Sanda na kasa Ibrahim K. Idris na shirya masa wata kitumura da nufin goga masa laifin da bai aikata ba domin bata masa suna.

Saraki ya bayyana hakan ne a zaman yau Laraba da majalisar dattawan ta yi a zaurenta dake babban birnin tarayya Abuja. Ya kara da cewar, ya samu labari daga majiya mai tushe, shi ne Gwamnan jihar Kwara Abdulfattai Ahmed.

Yace an shirya za’a dauki wasu mutane daga Kwara da ake bincike kuma aka same su da laifuka a kaisu zuwa birni tarayya Abuja, domin alakanta laifin da ake zarginsu da shi zuwa Bukola Saraki.

Bayan da Bukola Saraki ya gabatar da wannan jawabi a zauren majalisar dattawan, ya sauka daga kan kujerarsa, inda ya baiwa mataimakinsa Ike Ekweremadu damar cigaba da jagorantar  zaman majalisar.

LEAVE A REPLY