Lawal Daura

Rundunar tsaro ta farin kaya, DSS, ta karyata wani faifan bidiyo da ake yadawa a kafafen sadarwa na zamani, inda ake nuna cewar an samu wasu makudan kudade a gidajen tsohon Shugaban hukumar Lawal Daura dake Katsina da Abuja.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin Kakakin rundunar tsaro ta DSS, Tony Opuiyo, ya bayyana cewar, faifan bidiyon da yake nuna jami’an tsarona zakulo makudan kudade da suka kai Naira biliyan ashirin da daya da kuma wasu muggan makamai har guda dari hudu da kuma katunan zabe masu yawan gaske, wannan duk ba gaskiya bane, a cewar hukumar DSS.

 

LEAVE A REPLY