Mata biyu daga cikin 700 da Sojojin Najeriya suka kubutar daga hannun ‘yan Boko Haram, sun haihu lafiya a inda suke a karamar hukumar Munguno dake jihar Borno.

Mataimakin darakta a sashin yada labarai na rundunar sojojin Najeriya karkashin bataliya ta 8, Mista Timothy Antigha, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Mista Antigha, wanda Kanar ne a rundunar sojan, ya bayyana cewar mutum 700 da ‘yan Boko Haram suka suka sace suka yi garkuwa da su, rundunar sojon karkashin bataliya ta 242 taci nasarar kubuto da su.

Ya cigaba da cewar, mutanan da ‘yan Boko Haram din suka sace suka yi Garkuwa da su sun kunshi maza da mata da yara kanana, wadan da aka tilasta musu zama leburorin ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

Ya ce, mata biyu daga cikin wadan da aka sace din sun haihu lafiya lau, a inda ake ajiye da su bayan an kubuto da su daga hannun ‘yan Boko Haram din.

Kakakin rundunar sojin ya kara da cewar, a yunkurin rundunar sojojin na ganin sun dakile ayyukan ‘yan kungiyar ta Boko Haram, karkashin tsarin da akai masa take da ‘Operation Deep Punch II’ sun ci nasarar karya lagon ‘yan kungiyar ta Boko Haram, wanda hakan ne ya baiwa mutanan da aka yi garkuwa da su damar tserewa.

“Fiye da mutane 700 wadan da suka hada da masunta da manoma wadan da ‘ya ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kama suka yi garkuwa da su ne, suke musu aiki a gonakinsu suka ci nasarar tserewa zuwa wasu tsibirai dake tafkin Chadi har zuwa Munguno”

Kamar yadda kakakin rundunar ya fada, da yawan mutanan da ‘yan kungiyar suke tsare da su a wajen su, sun ci nasarar tserewa a lokacin da rundunar sojan najeriya take yi musu ruwan wuta a yankin Chikun Gudu da kuma Munguno.

NAN

LEAVE A REPLY