Hassan Y.A. Malik

Shedikwatar rundunar tsaro ta kasa ta bayyana cewa ta kashe jumillan Fulani Makiyaya 35 da ke addabar jihar Binuwai a karshen makon da ya gabata.

Daraktan yada labarai mai rikon kwarya na rundunar sojin Nijeriya, Birgediya John Agim  ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa rundunar sojin ta cafke wani shahararren dan daba mai suna Adamu Abdullahi a jihar Nasarawa, inda aka samu muggan makamai a tare da shi.

Sojin sun gudanar da wani kwanton bauna akan Fulani makiyaya a kauyukan Umaisha da Toto, inda suka kashe makiyayan da suka yi yunkurin kai hari a kan kauyukan a karshen makon da ya gabata.

Sun samu nau’ikan bindigu da alburusai a tare da makiyaya da suka hada da kirar gida da na waje.

Haka kuma rundunar sojan ta kara da fulani makiyaya a karamar hukumar Gwer ta jihar Binuwai a dai karshen makon.

Rundunar ta cimma makiyayan ne a kauyen Chetarer inda bayan fafatawa na lokaci kadan sai jirgin yakin sojin sama Nijeriya ya kawowa sojin kasa doki kuma nan take makiyaya 35 suka je kasa wasu da dama kuma suka tsira da raunikan harbin bindiga.

A wancan karawa ta soji da fulani makiyaya aka yi a karamar hukumar Gwer, soja guda ya rasa ransa, 2 kuma sun samu raunika.

Har ila yau, rundunar sojin, a wani fitar aiki da ta yi a jihar Nasarawa, ta cafke wani Musa Habu mai shekaru 32, inda ta same shi da karamar bindiga kirar gida da alburusai da wayar hannu kirar Tecno da kuma kudi N130.00.

Binciken da rundunar ta gudanar na sama-sama ya nua cewa Musa Habu na da alaka da wani gungu na ‘yan bindiga da ke aikata ta’asa. Tuni dai rundunar ta mika Musa Habu ga jami’an tsaro na farin kaya DSS don su ci gaba da bincike.

Aikin rundunar sojin Pperation Whirl Stroke bai tsaya nan ba sai da ta kai aikinta jihar Taraba, inda a can ta cafke wasu ‘yan bindiga su 8 dauke da bindiga kirar AK47 guda 2, K2 guda 1 da kuma wasu bindigu kirar gida da kuma tarin alburusai.

A tare da ‘yan bindigan guda 8 har ila yau an samu wayoyin hannu, layu, kambu da guru. Za a mika su da abinda ka kama su da su ga DSS don ci gaba da bincike.

 

LEAVE A REPLY