Hassan Y.A. Malik

Rundunar sojin Nijeriya ta Exercise AYEM AKPATUMA ( Atisayen Tseren Mage) a lokacin da suke faturu a yankin kauyen Gidan Kiya da ke a karamar hukumar Ibbi ta jihar Taraba ta yi nasarar kama wani fulani makiyayi dauke da karamar bindiga da kunshin alburusai.

Haka kuma dai, rundunar ta yi nasarar hana barkewar tashin hankali tsakanin mafarauta da makiyaya a karamar hukumar Obi ta jihar Nassarawa bayan da aka kirata ta zo shiga tsakani kungiyoyin biyu.

Kanal Aliyu yusuf, wanda ya yi magana a madadin daraktan hulda da jama’a ta rundunar sojin Nijeriya ya bayyana cewa, rundunar Atisayen Tseren Mage ta cafke wani fulani makiyayi dauke karamar bindiga kirar Hausa, da kuma kunshin alburusai, sai rigar silke da ke hana harsashi ya ratsa ya samu wanda aka harba da kuma adda.

Kanal Aliyu ya ce, tuni dai suka mika makiyayin a hannun ‘yan sanda don su ci gaba da bincike.

Ya ci gaba da cewa rundunar Atisayen Tseren Mage na samun nasara yadda ya kamata. Amma kuma suna kira ga jama’ar yankin da suke aiki da su basu hadin kan da ya kamata don tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kanal Aliyu ya bukaci da al’umma ta sanar da rundunar duk wani abu da hankalinsu bai kwanta da shi ba don daukar mataki cikin gaggawa don gudun kar har sai barna ta faru kafin a hukuma ta kai ga sanin abinda ake ciki.

LEAVE A REPLY