Hassan Y.A. Malik

 

Wani Soja ya bindige matarsa kafin daga bisani ya kasha kansa bayan da ya fahimci cewa ‘ya’ya biyun da yak e zaton nasa ne da matar tasa ta Haifa mas aba shi  ne mahaifinsu ba.

 

Wannan soja mai suna Pathias Mwape na zaune a wani barikin sojoji da ke a kasar Zambia, inda a nan cikin barikin ne ma matar Pathias din ta kulla mumunar alaka da abokin mijinta, wanda da shi ne ma ta samu ‘ya’ya biyun da mijinta ya raina a matsayin ‘ya’yansa na jini. 

 

Rahotonni sun bayyana, sojan ya tunkari matarsa da bindiga don tabbatar da labarin da ya jiyo daga ‘yan unguwa na cewa ba shine uban ‘ya’yan da ya share shekara da shekaru yana rainonsu ba.

 

Haduwarsu da matar ke da wuya sai ta sanar masa cewa hakika ba shi bane mahaifin yaran, abokin aikin sa ne mahaifinsu. A nan take sojan ya harbe ta da bindiga har lahira kana daga baya ya kashe kansa yayin da ya ji labari cewa yan sanda na neman sa ruwa a jallo.

 

LEAVE A REPLY