Majalisar Shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa ta rubuta wasika ga majalisar dokokin jihar inda take neman a sake yiwa dokar da ta kafa majalisar kananan hukumomi a yi mata garambawul ta hanyar tsawaita musu wa’adin mulki.

Shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa dai na yin wa’adin mulki na shekaru biyu ne kacal bayan sun sha rantsuwar kama aiki a matsayin zababbun Shugabannin, a yayin da wa’adinsu yake karewa anan da mako biyu mai zuwa, Shugabannin sun bukaci a yiwa dokar garambawul da zata tsawaita wa’adin mulkinsu.

Sai dai kuma, wani lauya mai zaman kansa a Yola babban birnin jihar Adamawa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, cewar duk wani yunkuri da majalisar dokokin jihar zata yi domin cimma wancan bukatun na Shugabannin kananan hukumomin ya sabawa dokar kasa.

 

LEAVE A REPLY