Allah ya yiwa Shugaban majalisar Malamai na jihar Kaduna Sheikh Abubakar Usman Baban Tune rasuwa a ranar Litinin.

Sheikh Baban Tune shi ne Shugaban majalisar Malamai da Limamai ta jihar Kaduna kuma shi ne babban Limamin NNPC.

Ya rasu bayan ya sha fama da jinya. Sheikh Dr. Ahmad Gumi be ya sanar da rasuwar Malamin a shafinsa na Facebook. Allah ya jikansa.

LEAVE A REPLY