Tanimu Turaki da Sule Lamido da Atiku Abubakar da kuma Malam Ibrahim Shekarau

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus tare da tsohon Shugaban kasa Atiku Abubakar  da Malam Ibrahim Shekarau da Sule Lamido da Kabiru Tanimu Turaki da kuma Attahiru Bafarawa sun isa jihar Sakkwato domin jajantawa Gwamnati da al’ummar jihar  Sakkwato bisa abinda ya faru a makon jiya na kashe kashe da aka yi a jihar.

Yayin ziyarar sun bayyana sakon magoya bayan jam’iyyar PDP a duk fadin Najeriya bisa wannan ibtila’i da ya faru a jihar ta Sakkwato, tare da adduar Allah ya jikan wadan da suka rasu ya baiwa wadan da suka jikkata lafiya.

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya nuna jin dadinsa da wannan ziyara ta zumunci da ‘yan uwantaka, tare kuma da bayyana godiyar mutanan jihar Sakkwato bisa wannan muhimmiyar ziyara ta alhinida jajantawada aka kawo musu.

LEAVE A REPLY