Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu

Wasu mahara da ba’a san ko su waye ba, sun kai hari gidan Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, a daren jiya inda suka kashe wani dan sanda guda daya. Inda kuma suka yi arba da wani ma’aikaci shima daure shi.

Kusan wannan shi ne, karo na uku a jere da ake kai hari ga Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu,inda ake neman rayuwarsa ko ta wanne hali. ‘Yan sanda dai na ci gaba da gudanar da bincike kan wannan hari da aka kaiwa Magu.

Sai dai har ya zuwa yanzu Magu ko masu magana da yawun EFCC babu wanda yace uffan kan wannan batu. Haka kuma, ana zargin maharan sun ci nasarar tserewa da wasu kayayyaki a gidan Shugaban EFCC din da suka shiga, ba a kai ga bayyana irin abubuwa da maharan suka dauka ba.

Sai dai ana zargin daga cikin abin da suka dauka har da wasu dabbobi da suka kunshi Shanu da Awaki da suke harabar gida, a yayin da suka shiga.

Muna jiran jin ko hukumar EFCC zata fitar da wani bayani kan wannan batu.

LEAVE A REPLY